Rooney da Martial za su yi jinya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wayne Rooney ba zai samu buga wasan da za a yi da Watford ba saboda rashin lafiya.

Kociyan Manchester United Louise Van Gaal, ya ce Anthony Martial da Wayne Rooney na cikin 'yan wasa shida da ba za su buga wasan da kulob din zai yi da Watford FC ranar Asabar ba.

Martial, mai shekaru 19, ya samu rauni a wasan sada zumunta da Faransa ta buga da Ingila ranar Talata, shi kuwa Rooney yana fama ne da rashin lafiya.

Michael Carrick ma ya yi rauni a karawar da Ingila ta yi da Spaniya, inda zai bi sahun Marouane Fellaini da Antoni Valencia da Luke Shaw da suke jinya.

Van Gaal ya ce James Wilson ba shi da kuzarin da zai iya kwashe minti 90 yana murza leda.

An zargi Manchester United da rashin kuzari a kakar wasa ta bana, kuma su ne ke da mafi karancin kwallaye cikin kulob bakwai da ke saman tebir a gasar Premier.