Barcelona ta casa Real Madrid da ci 4-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona tana mataki na daya a kan teburi da maki 30

Barcelona ta doke Real Madrid da ci 4-0 a wasan hamayya a gasar cin kofin La Liga wasan mako na 12 da suka kara a Bernabeu.

Tun a minti na 11 da fara tamaula ne Suarez ya ci wa Barcelona kwallon farko, sannan Neymar ya kara ta biyu saura minti shida a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hudun Iniesta ya kara ta uku, kuma Suarez ya kara cin ta hudu kuma kwallo ta biyu da ya ci a wasan.

Real Madrid ta karasa karawar da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Isco jan kati bisa ketar da ya yi wa Neymar daf da za a tashi daga wasan.

Wannan shi ne karon farko da Real Madrid ta yi rashin nasara a wasan La Liga biyu a jere a bana, a ranar 8 ga watan Nuwamba Sevilla ce ta ci Madrid 3-2.

Barcelona ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburi da maki 30, a inda Real Madrid ta hada maki 24 daga wasanni 12 da ta yi.