Chelsea ta ci Norwich City daya mai ban haushi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea ta koma mataki na 15 a kan teburin Premier

Chelsea ta doke Norwich City da ci daya mai ban haushi a wasan Premier ta mako na 13 da suka kara a Stamford Bridge a ranar Asabar.

Diego Costa ne ya ci wa Chelsea kwallon kuma ta farko da ya zura a raga tun wacce ya ci a wasanni bakwai baya da ya buga.

Chelsea ta hada maki 14 daga wasanni 13 da ta buga a gasar Premier, za kuma ta fafata ne da Tottenham a wasan mako na 14 da za ta yi.

Norwich kuwa za ta kara ne da Arsenal wacce ta yi rashin nasara a hannun West Brom da ci 2-1 a ranar Asabar.

Ga sakamakon wasu wasannin da aka buga:

  • Watford 1 - 2 Man Utd
  • Chelsea 1 - 0 Norwich
  • Everton 4 - 0 Aston Villa
  • Newcastle 0 - 3 Leicester
  • Southampton 0 - 1 Stoke
  • Swansea 2 - 2 Bournemouth
  • West Brom 2 - 1 Arsenal