Manchester United ta ci Watford 2-1

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United ta hada maki 27 daga wasanni 13 da ta yi a gasar Premier

Manchester United ta ci Watford 2-1 a gasar Premier wasan mako na 13 da suka kara a ranar Asabar a filin wasa dake titin Vicarage.

United ce ta fara cin kwallo ta hannun Memphis Depay, wanda rabonsa da murza leda tun ranar hudu ga watan Oktoba sakamakon raunin da ya ji.

Saura minti hudu ya rage a tashi daga wasan Etienne Capoue ya farke kwallon da aka ci Watford daga bugun fenariti.

Daf kuma da za a tashi ne Bastian Schweinsteiger ya ci wa United kwallo ta biyu, bayan da ya samu tamaula daga bugun da Jesse Lingard ya yi wo masa ta kuma bugi jikin Deeney ta fada raga.

Da wannan sakamakon United ta hada maki 27 daga wasanni 13 da ta buga, za kuma ta kara da PSV a gasar cin kofin zakarun Turai a wasanta na gaba.