'Yan wasan Arsenal da dama na yin jinya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Talata ce Arsenal za ta kara da Dinamo Zagreb

Arsenal na fama da tarin 'yan wasanta da suke yin jinya a shirin da take yi na karawa da Dinamo Zagreb a gasar cin kofin zakarun Turai a ranar Talata.

Dan kwallon Arsenal mai wasan tsakiya Francis Coquelin da kuma Mikel Arteta sun ji rauni a wasan da West Brom ta ci Arsenal 2-1 a gasar Premier ranar Asabar.

Arsenal tana da maki uku kacal a rukuni na shida, kuma tana da bukatar doke Zagreb da hakan zai iya bata damar kai wa wasan zagaye na biyu a gasar.

A gasar Premier da Arsenal ta yi a ranar Asabar, Aaron Ramsey da Danny Welbeck da Theo Walcott da kuma Alex-Oxlade Chamberlain ba su buga mata karawar ba, bisa jinya da suke yi.

Tun a ranar Juma'a Wenger ya ce yana sa ran Ramsey zai buga wasan cin kofin zakarun Turai da za su yi a ranar Talata, yayin da sai a ranar Lahadi ake sa ran Chamberlain zai buga wasan Premier da Norwich.