Ba za mu manta doke Madrid da muka yi ba - Enrique

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Barcelona ce ta doke Real Madrid 4-0 a wasan gasar La Liga na mako na 12

Kociyan Barcelona, Luis Enrique ya ce za a dade ba a manta da cinye Real Madrid 4-0 a gasar La Liga da suka yi a ranar Asabar a Bernabeu ba.

A karawar da suka yi wacce ake yi mata lakabi da El Clasico Luis Suarez ne ya ci biyu sannan Neymar da kuma Andres Iniesta kowannensu ya ci kwallo guda-guda.

Sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Barcelona ta saka Messi a wasan da Madrid ta karasa shi da 'yan wasa 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Isco jan kati daf da za a tashi daga kwallon.

Enrique ya ce "Nasarar da muka samu mai faranta rai ce, saboda abokan hamayya muka doke a gidansu".

Barcelona ce ta fi rike kwallo a karawar, kuma ta samu damar-makin zura kwallaye da yawa a raga a fafatawar.

Barca ta na nan a matakinta na daya a kan teburi da maki 30, yayin da Rel Madrid ke biye da ita da maki 24 bayan da suka yi wasanni 12 a gasar La Liga.