Man United na son ta sayo Ronaldo - Van Gaal

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Real Madrid ta yi rashin nasara a wasa biyu a jere a gasar La Liga

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal ya tabbatar da cewar yana son ya dawo da Cristiano Ronaldo Old Trafford ya buga tamaula.

Ronaldo dan kasar Portugal, ya bar United a shekarar 2009 a inda ya koma Real Madrid kan kudi £80m.

An dade ana ta jita-jiar cewar dan wasan mai shekara 30 da haihuwa na daf da barin Real Madrid.

Van Gaal ya kara da cewar "Muna son dauko 'yan wasa da dama, ba kawai Ronaldo ba, amma da kyar idan za a iya sayar mana da su, kan Ronaldo muna saurare da kuma fata."

Ronaldo gwarzon dan kwallon kafa na duniya karo uku, ya kafa sabon tarihin yawan ci wa Madrid kwallaye, inda ya doke Raul wanda ya ci 323 a baya.

A shekara shida da yake buga wa Madrid tamaula ya lashe kofin La Liga dana zakarun Turai da Spanish Cup guda biyu.

Kafin ya bar United ya dauki kofunan Premier Uku da kofin zakarun Turai dana FA da kuma League Cup a shekara shida da ya yi a Old Trafford.