Tottenham ta yi wasanni 12 a jere ba a doke ta ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption karo na biyu kenan da Tottenham ta buga wasanni 12 ba tare da an doke ta ba

Totteham ta ci West Ham United 4-1 a gasar Premier wasan mako na 12 da suka kara a White Hart Lane a ranar Lahadi.

Kane ne ya fara ci wa Tottenham kwallon farko kuma ta biyar da ya zura a wasanni biyar da ya buga, sannan Toby Alderweireld ya kara ta biyu daga bugun kwana da ka.

Kane din dai shi ne ya ci ta uku sannan kuma Walker ya zura ta hudu a raga, daga nan ne West Ham ta zare kwallo daya ta hannun Lanzini.

Da wannan nasarar Tottenham ta kafa tarihin buga wasanni 12 a jere ba tare da an doke ta ba a karo na biyu, kuma tana mataki na biyar a kan teburi da maki 24.

West Ham kuwa tana matsayi na shida ne da maki 21 a kan teburin na Premier.