Ba zan koma Gasar Premier ba - Gareth Bale

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gareth Bale tsohon dan kwallon Tottenham ne

Dan kwallon Real Madrid, Gareth Bale, ya ce ba ya tunanin cewar zai sake komawa buga wasa a Gasar Premier.

Bale, dan wasan tawagar kwallon kafar Wales, ya buga wasan El Clasico da Barcelona ta doke su da ci 4-0 a ranar Asabar a wasan La Liga.

Dan kwallon wanda ya koma taka leda Madrid kan kudi £85m daga Tottenham, ya ci mata kwallaye 30 a wasanni gasar La Liga 65 da ya yi, sai dai kuma rabon da ya zura kwallo a raga tun a cikin watan Agusta.

Bale ya ce, "Tun lokacin da na fara buga tamaula fatana bai wuce na kai kololuwa a wasan ba, kuma Real Madrid ce karshen tamaula".

Ya kuma kara da cewa "Ba zan ce ba zai yi wu na sake komawa can da taka leda ba, saboda ba a san abin da gaba za ta haifar ba".

Jaridu da dama sun wallafa cewar Bale zai koma murza leda A gasar Premier kuma a Manchester United.