U-23: Siasia ya fitar da 'yan wasa 21

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe uku ne za su wakilici Afirka a wasan Olympics da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa

Kociyan tawagar kwallon kafa ta matasa 'yan kasa da shekaru 23 ta Nigeria, Samson Siasia, ya fitar da sunayen 'yan wasa 21 da za su wakilici kasar a Senegal.

Senegal ce za ta karbi bakuncin wasannin Afirka na neman tikitin shiga wasan kwallon kafa na Olympics da za a yi a Brazail a shekara mai zuwa.

Za a fara wasannin ne daga ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba, kuma za a fafata a filayen wasa na Dakar da kuma M'bour, kuma kasashe uku ne za su wakilci Afirka.

Ga sunayen 'yan wasa 21 da Siasia ya sanar:

Masu tsaron raga: Yusuf Mohammed (Kano Pillars), Emmanuel Iwu (Heartland), Emmanuel Daniel (Enugu Rangers)

Masu tsaron baya: Zaharadeen Bello (Kano Pillars), Seun Olubayo (Sunshine Stars), Chizoba Amaefule (Dolphins), Ebuka Iroha (Diamond Football Academy), Sincere Seth (Supreme Court FC), Seun Oduduwa (Nath Boys)

Masu buga tsakiya:Azubuike Okechukwu (Yeni Matalatyaspor, Turkiy), Godspower Aniefiok (Kano Pillars), Ndifreke Effiong (Abia Warriors), Usman Mohammed (FC Taraba),Tiongoli Tobara (Bayelsa United), Bature Yaro (Nasarawa United), Oghenekaro Etebo (Warri Wolves), Stanley Dimgba (Warri Wolves)

Masu zura kwallo a raga: Taiwo Awoniyi (FSV Frankfurt, Germany), Isaac Success (Granada CF, Spain), Junior Ajayi (CS Sfaxien, Tunisia), Kufre Ebong (Warri Wolves)