Kofin Davis: Tawagar Burtaniya ta gamsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A karshen mako tawagar Burtaniya za ta buga wasan karshe na Gasar Kofin Davies

Tawagar Burtaniya a gasar tennis ta cin Kofin Davis ta ce ta gamsu da matakan tsaron da aka dauka a garin Ghent na kasar Belgium, inda za ta buga wasan karshe a karshen mako. Dan wasan tennis na daya a Burtaniya, Andy Murray, ne ya bayyana hakan.

Har yanzu akwai tsauraran matakan tsaro a babban birnin kasar ta Belgium, wato Brussles, mai nisan kilomita 35 daga Ghent, saboda barazanar kai hare-hare irin wadanda aka kai Paris da yake fuskanta.

Ranar Litinin tawagar ta Burtaniya ta isa Ghent, kwana guda kafin ranar da aka shirya tun farko, bayan da aka tabbatar da kammala shirye-shiryen tsaro.

A cewar Murray, "Ina jin kowa a tawagar hankalinsa a kwance yake".

Ya kara da cewa, "A 'yan kwanakin da suka gabata hankali ya dan tashi, amma zuwanmu nan, bayan mun shiga otal mun kuma ziyarci filin wasan mun ga abubuwan da aka tanada, a ganina ya kwantar da hankula".

Tawagar ta kunshi Murray, da dan uwansa Jamie, da Kyle Edmund, da James Ward da kuma Dom Inglot.