Ana zargin shugaban IAAF da son-kai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lord Coe ya ce shi bai kama kafa a wajen kowa ba

Shugaban hukumar kula da guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, IAAF, Lord Sebastian Coe, na fuskantar zargin bin son zuciya bayan da wadansu sakonnin email suka bayyana, wadanda ke nuni da cewa ya yi kamun kafa a wajen wanda ya gada don neman damar karbar bakuncin gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta 2021.

Birnin Eugene na Amurka aka baiwa damar karbar bakuncin gasar ba tare da an gudanar da zabe ba, duk da cewa birnin Gothenburg na Sweden ma ya nemi a ba shi damar shirya gasar.

Wani bincike da BBC ta gudanar ya bankado sakonnin na email wadanda suka yi ikirarin cewa Coe, wanda wakili ne na kamfanin Nike, kuma a lokacin shi ne mataimakin shugaban hukumar IAAF, ya "tuntubi" Lamine Diack don ya mara baya ga bukatar Eugene.

Birnin na Jihar Oregon, wanda ya birnin Doha ya kayar a neman damar shirya gasar 2019, yana da alaka ta kut-da-kut da kamfanin Nike.

Jagoran neman damar daukar nauyin gasar a madadin Gothenburg, Bjorn Eriksson, ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a yi bayani game da wannan zargi na son-kai.

Sai dai Lord Coe ya shaida wa BBC cewa shi bai kama kafar kowa ba.