Kila a yi wa Platini haramcin har-abada

Image caption Ana zargin Blatter da bai wa Platini wata kwangila da ba ta amfani FIFA ba

Mai yiwuwa a haramta wa Michel Platini, mataimakin shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, shiga harkar wasan kwallon kafa har tsawon rayuwarsa.

Lauyan Mista Platini, Thibaud d'Ales, wanda ya bayyana hakan, ya kwatanta shawarwarin da kwamitin da'a na hukumar ta FIFA ya bayar—wadanda ya kira "masu tsauri fiye da kima"—da cewa "abin kunya" ne.

A yanzu haka dai an dakatar da shugaban na Hukumar Kwallon Kafa ta Turai, UEFA, shi da shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter, a bisa tuhumar tafka almundahana.

Tuni mutanen biyu suka musanta cewa sun aikata laifi.

A watan gobe ne dai kwamitin ladbatarwa na hukumar ta FIFA zai yanke hukunci a kan shawarwarin kwamitin da'ar.

Karin bayani