An sauya lokacin wasan Zakarun Afirka

Hakkin mallakar hoto caf
Image caption Kungiyar Orlando Pirates ta AFirka ta Kudu ta ce ta gamsu da shawarar da CAF ta yanke

An sauya lokacin da ya kamata a fara wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Afirka, wanda za a buga ranar Lahadi a Tunisia.

Mummunan harin bam din da aka kai a Tunis, babban birnin kasar ta Tunisia, ranar Talata shi ne ya sa aka yi sauyin.

A yanzu dai kungiyar kwallon kafa ta Etoile Du Sahel za ta karbi bakuncin Orlando Pirates ta Afirka ta Kudu ne a birnin Sousse, da karfe biyu na rana a gogon GMT a maimakon karfe shida da rabi na yamma, agogon GMT.

Etoile ce ta bukaci sauyin bayan da aka ayyana dokar hana fitar dare a daukacin kasar ta Tunisia.

Kungiyar ta Orlando Pirates ta ce duk abin da CAF ta yanke a kan lamarin ya yi daidai.

A zagaye na farko na wasan da aka buga ranar Asabar a Soweto, ko wacce daga cikin kungiyoyin na da ci daya.

Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, wacce ta ce za a buga wasan duk da kai harin, ta ce ta tuntubi hukumar kwallon kafa ta Tunisia da ma gwamnatin kasar kafin ta yanke shawara.

Karin bayani