Abin da ya sa nake son Senegal —Diao

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Keita Diao bai taba buga wa Senegal ba, amma ya ji dadi da ta tuntube shi

Dan wasan Lazio, Keita Balde Diao, ya shaida wa BBC cewa ta hanyar buga wa Senegal kwallo zai iya zama kasaitaccen dan wasa, don haka ya zabi ya buga wa tawagar Teranga Lions a kan tawagar Spaniya.

A Spaniya aka haifi dan wasan mai shekaru 20, amma yana da damar buga wa Senegal, kasar iyayensa ta asali.

Ko da yake kungiyar da yake takawa leda a Italiya ba ta kyale shi ya je ya buga wasan neman gurbi a gasar Olympic mai zuwa zuwa ba, dan wasan na fatan taka leda a Rio idan Senegal ta samu tikitin.

"Babu shakka zan rika bibiyar sakamakon wasannin, da fatan za mu kai gaci", inji Keita Balde Diao.

Ranar 28 ga watan Nuwamba za a fara Gasar cin Kofin Kasashen Afirka ta 'yan kasa da shekara 23, wacce kasashe takwas za su buga don neman tikitin shiga Gasar Olympics.