Chelsea: Mourinho da Costa sun sasanta

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mourinho bai ji dadin babakeren da Costa ya yi a wasansu da Maccabi Tel Aviv ba

Kocin Chelsea, Jose Mourinho, ya ce shi da Diego Costa sun shirya bayan wata sa-in-sa da suka yi yayin wasansu na Gasar cin Kofin Zakarun Turai da Maccabi Tel Aviv ranar Talata, wanda suka lashe da ci 4-0.

Mourinho bai ji dadin yadda dan wasan da Spaniya ya rika kokarin yin babakere a rabin lokaci na farko na wasan.

Costa, wanda ya wasansa na shida da ya buga ba tare da ya ci kwallo ba shi ne wasan da suka buga da Norwich ranar Asabar, ya buga wasan na ranar Talata har karshe.

A cewar Mourinho, "Ban ji dadi ba, don haka na harzuko, shi ma ya harzuko. Amma da aka tafi hutun rabin lokaci mun rungumi juna mun sasanta".

Nasarar da Chelsea ta yi ta ba ta damar haurawa saman Rukunin G da maki 10 tare da Porto.

Karin bayani