Shugaban IAAF ya yanke alaka da Nike

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Lord Sebastian Coe ya kuma ce Rasha ta amince da dakatar da ita da IAAF ta yi

Shugaban hukumar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, IAAF, Lord Sebastian Coe, ya kawo karshen rawar da ya yi shekaru 38 yana takawa a matsayin wakilin kamfanin Nike.

Wannan mataki ya biyo bayan zargin da aka yi ne na nuna son-kai wajen bai wa birnin Eugene damar daukar nauyin Gasar Guje-Guje ta 2021.

Birnin na Eugene da ke Jihar Oregon a Amurka ne dai hedkwatar kamfanin Nike, mai yin kayan wasanni.

Kwamitin zartarwa na hukumar ta IAAF ya ce Coe zai iya ci gaba da rike mukamin wakilin na Nike, amma Coe din ya ce yin hakan zai dauke masa hankali daga aikin tafiyar da hukumar, lamarin da ke bukatar aikin sa'o'i 18 a kullum.

Wannan zargi dai na zuwa ne yayin da a baya-bayan nan hukumar ta IAAF ta fuskanci wata badakala ta amfani da kwayoyi masu kara kuzari, wacce Coe ya sha alwashin kakkabewa.

Coe ya kuma sanar da cewa zai yi murabus daga shugabancin Hukumar Wasannin Olympic ta Burtaniya bayan kammala gasar ta Olympics ta 2016 a Rio de Janeiro.

Wani bincike da BBC ta gudanar a wannan makon ya bankado wadansu sakonnin email da ke nuni da cewa lokacin yana rike da mukamin mataimakin shugaban IAAF, Coe ya kama kafa a wajen tsohon shugaban hukumar, Lamine Diack, don ya bai wa birnin Eugene goyon baya.

Karin bayani