Didier Drogba zai koma Chelsea

Hakkin mallakar hoto
Image caption Har yanzu ba a tantance rawar da Didier Drogba zai taka ba idan ya koma Chelsea

Tsohon kyaftin din Ivory Coast, Didier Drogba, ya ce tuni ya cimma wata yarjejeniya ta komawa tsohuwar kungiyarsa Chelsea idan ya daina taka leda.

Har yanzu dai ba a yanke shawara a kan hakikanin rawar da dan wasan mai shekaru 37 zai taka ba.

Sai dai an ambato shi yana cewa, "Me zai hana na zama manaja, ko daraktan wasanni, ko mai bayar da horo a makarantar koyon kwallo, ko kuma mai bayar da shawara ga 'yan wasan gaba?"

A yanzu haka dai Drogba na wasa ne a kungiyar Montreal Impact ta Canada.

Karin bayani