FIFA ta ba da agajin agoguna 48

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Kwamitin da'a na FIFA ya ce ba za a ladabtar da kowa ba matukar an mai da agogunan

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta ce ta bayar da gudunmawar wadansu agoguna na kawa guda 48 ga wata kungiyar bayar da agaji wacce ayyukanta suka jibinci harkar kwallon kafa a Brazil.

Jami'an hukumar kwallon kafa ta Brazil ne suka bai wa jami'an FIFA da shugabannin hukumomin kwallon kafa na wadansu kasashe kyautar agogunan samfurin Parmigiani.

Kwamitin da'a na hukumar FIFA ya yanke hukunci cewa kyautar agogunan ba ta kan ka'ida, amma ba za a dauki matakin ladabtarwa ba a kan duk wanda ya mayar da su.

An kiyasta cewa farashin ko wanne daya daga cikin agogunan ya kai $24,500.