An zabi fitattun 'yan wasa 55 na duniya

Image caption Wannan ne karo na farko da 'yan FIFPro 25,000 suka kada kuri'a

Kungiyar Kwararrun 'Yan Wasan Kwallon Kafa ta Duniya, FIFPro, da hadin gwiwar Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta fitar da jerin sunayen 'yan wasa 55 wadanda za a zabi fitattun 'yan wasa 11 na 2015 daga cikinsu.

Dan wasan Ivory Coast da Manchester City, Yaya Toure, shi ne kadai dan Afirka da sunansa ya fito a jerin, wanda kwararrun 'yan wasa 25,000 a fadin duniya suka zaba.

'Yan wasan Gasar Premier 10 ne a cikin sunayen; yayinda a kungiyoyi 'yan wasan Real Madrid ne suka fi yawa—'yan wasanta 12 ne sunayensu suka fito a jerin.

A watan Satumba aka fara kada kuri'a, kuma 'yan wasan da suka buga wasanni akalla 15 a bana ne kawai suka cancanci shiga jerin.

A watan Janairu za a sanar da fitattun 'yan wasan 11 na duniya, a lokacin da za a bayyana wanda ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta duniya, wato Ballon d'Or.