Faransa: Ba tafiye-tafiyen kallon wasa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba dama 'yan kallo a Faransa su tafi wani gari don mara wa kungiyoyinsu

Za a haramta wa magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa na Faransa yin tafiye-tafiye zuwa wadansu garuruwa don kallon wasannin kungiyoyin nasu daga yanzu har zuwa tsakiyar watan Disamba.

Za a dauki matakin ne dai saboda ayyana dokar ta-baci sakamakon hare-haren da aka kai Paris da kuma Babban Taron Sauyin Yanayi da za a gudanar a birnin.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ambato wata sanarwa da hukumar kula da gasar wasannin kwallon kafa na Faransa ta fitar tana cewa, "Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta bayar da umarnin hana 'yan kallo tafiya wasu garuruwa don kallon wasannin zagaye na 15 na wasannin gasar Ligue 1 da zagaye na 16 na wasannin gasar Ligue 2 a karshen wannan makon".

Sanarwar ta kuma ce nan ba da jimawa ba za a bayar da wani umarnin na haramta tafiye-tafiye don kallon zagaye na 16, da na 17, da na 18 na wasannin gasar Ligue 1, da Ligue 2, da zagaye na takwas na Gasar cin Kofin Faransa, da kuma wasannin gasar Europa League.

Karin bayani