Celtic ta fice daga gasar Europa

Image caption Celtic ta fice daga gasar Europa, bayan da Ajax ta lallasa ta da ci 2-1 ranar Alhamis.

Ranar Alhamis ne Ajax ta lallasa Celtic da ci 2-1 a gasar Europa.

Celtic din ta fara da zafi zafinta, inda Callum Mcgregor soma zura kwallo minti uku da fara wasa.

Bayan haka Ajax ta rama bayan sakacin da Arkadiusz Milik ya yi.

Celtic ta kara matsa kaimi daga karshe amma Leigh Griffiths da Charlie Mulgrew suka bai wa Vaclav Cerny damar zira kwallon Ajax ni biyu.

Wannan kashi da Celtic ta sha ne ya fitar da su daga gasar ta Europa, inda suke kasan teburin da maki biyu kacal.