Ba za mu sayar da Sadio Mane ba — Koeman

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gabannin radi radin da ake yi cewa Manchester za ta sayi Sadio Mane, kociyan Southampton din ya jadda cewa basu shirya sayar da dan wasan ba.

Kociyan Southhampton Ronald Koeman ya kara jaddada cewa kulob din bai shirya sayar da dan wasa Sadio Mane ba.

Kociyan yana kan bakansa cewa ba zai sayar da dan wasan ba tun watan Agusta, inda ya ce ba za su sayar da kowanne dan wasa a watan Janairu ba, lokacin da cinikin 'yan kwallo.

Ya ce, "Duk masu neman su sayi Sadio daga Manchester da Chelsea, ku sani cewa ba za mu sayar da kowanne dan wasanmu a watan Janairu ba".

Koeman, mai shekaru 52, ya ce gasar zakarun Turai ita ce muhimmin abin da ke sa 'yan wasa su kara kaimi a kulob-kulob din da ke tsaka-tsaki.