Daniel Sturridge ya yi rauni a kafa

Hakkin mallakar hoto Daniel Sturridge
Image caption Sturridge ya yi korafin cewa baya jin karfin kafarsa.

Watakila dan wasan Liverpool Daniel Sturridge zai sake yin jinya bayan raunin da ya yi a kafarsa a lokacin da suke yin atisaye.

Wannan rauni zai hana shi murza leda a karawar da Liverpool din ke shirin yi da Bordeaux a gasar cin kofin Europa.

Sturridge -- mai shekaru 26 -- ya yi fatan dawowa filin kwallon ranar Alhamis bayan jinyar da ta hana shi murza leda tun ranar hudu ga watan Oktoba, amma sai ga shi an sake tura shi gwaji asibiti bayan ya yi korafin rashin jin karfin kafarsa.

Sturridge ya buga wasa sau uku ne kacal a kakar wasanni ta bana kuma sau 18 ya murza leda a kakar wasa ta shekarar 2015.