Vardy ya kafa tarihin cin kwallaye a wasanni 11 a jere

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester tana mataki na biyu a kan teburi da maki 29

Dan kwallon Leicester City, Jamie Vardy ya kafa tarihin yawan cin kwallaye a wasanni 11 da ya yi a jere a gasar Premier Ingila a bana.

Dan wasan ya kafa tarihin ne bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 a karawar da suka yi da Manchester United a gasar Premier wasan mako na 14 a ranar Asabar.

United ta farke kwallon da aka zura mata ne ta hannun Schweinsteiger daf da za a tafi hutun rabin lokaci.

Tsohon dan wasan Manchester United, Ruud van Nistelrooy shi ne yake rike da tarihin a baya, inda ya ci kwallo a dukkan wasanni 10 da ya buga a jere a kakar wasan 2003.

Vardy shi ne ke kan gaba a matsayin dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar Premier inda ya zazzaga 14 a raga.