Na kusa yin ritaya daga damben gargajiya - Horo

Image caption Ashiru Horo sarkin damben gargajiya daga bangaren Arewa

Sarkin dambe Ashiru Horo ya ce ya kusa ya yi ritaya daga yin wasan damben gargajiya, sakamakon rashin abokan karawa a wasan.

Horo ya yi wannan jawabin ne a lokacin da ake yi masa ajo a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria a ranar Lahadi da safe.

Dan damben wanda ke kare martabar Arewa ya kara da cewar da zarar ya samu mai gida da zai dauki nauyinsa, daga nan ne zai yi bankwana da wasan damben gargajiya.

Sarkin dambe Horo ya godewa dukkan jama'ar da suka halarci ajonsa, ya kuma ce zai cigaba da rike sarautar damben gargajiya da ya dade yana rike da ita.

Ga sakamakon wasannin da aka yi kuma babu kisa a fafatawar:

  1. Garkuwan Mai Caji daga Kudu da Tufak daga Arewa
  2. Shagon Mada daga Kudu da Dogon Na Manu daga Arewa
  3. Shagon Bahagon Musan Kaduna Arewa da Shagon Autan Sikido Kudu
  4. Autan Faya daga Kudu da Shagon Audu Argungu daga Arewa
  5. Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Shagon Shagon Alhazai daga Arewa
  6. Autan Faya daga Kudu da Shagon Bahagon Roget daga Arewa