Zan sake dambatawa da Furu a 2016 - Klitschko

Image caption Fury ya ce yana fatan shi ma zai kare kambunan da ya lashe zuwa tsawon lokuta

Wladimir Klitschko ya ce zai sake yin dambe da Tyson Fury a shekara mai zuwa, bayan da ya yi rashin nasarar kumbunansa na damben boksin da suka kara a Dusseldorf a ranar Asabar.

Fury, mai shekaru 27, ya kawo karshen rike kambunan da Klitschko dan kasar Ukraine ya rike na tsawon shekaru tara ba tare da an doke shi ba a damben boksin.

Klitschko mai shekaru 39, ya ce "Tabbas an doke ni, amma har yanzu akwai dambe a tare da ni, za mu tsayar da ranar da za mu sake yin wasa da wurin da ya kamata mu fafata".

Fury ya mai da martani da cewar "ni dan dambe ne a shirye nake na amsa kalubale, ina son na zama fitatcen dan wasa a duniya, kuma za mu sake karawa, damben zai yi zafi".

Fury ya lashe kambun WBA da IBF da kuma WBO daga hannun Klitschko, rabon da a doke shi tun a 2004, bayan da ya sha kashi a hannun Lamon Brewster.