Tottenham da Chelsea sun tashi Canjaras

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea ta koma mataki na 14 a kan teburin Premier

Tottenham da Chelsea sun tashi canjaras a gasar Premier wasan mako na 14 da suka kara a filin wasa na White Hart Lane a ranar Lahadi.

Wasan dai na hamayya ne, domin kungiyoyin biyu suna zaune a birnin Landan ne, kuma fafatawar ba ta kayatar ba kamar yadda aka za ta tun da fari.

Da wannan sakamakon Chelsea ta matsa sama zuwa mataki na 14 a kan teburin Premier da maki 15, a inda Tottenham ta ci gaba da zama a matakinta na biyar a kan teburin da maki 25.

Tottenham za ta ziyarci West Brom a gasar mako na 15, ita kuwa Chelsea za ta karbi bakuncin Bournemouth a Stamford Bridge a ranar 25 ga watan Disamba.