U-23: Nigeria ta doke Mali da ci 3-2

Hakkin mallakar hoto theNFF Twitter
Image caption Nigeria za ta kara a wasa na biyu ne da Masar a ranar Laraba

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria ta matasa 'yan kasa da shekara 23 ta doke ta Mali da ci 3-2 a gasar cin kofin matasa ta Afirka, domin neman gurbin shiga wasannin Olympics.

Tun kafin aje hutun rabin lokaci ne Nigeria ta zura kwallayenta uku a ragar Mali wacce ta zare guda biyu da aka zura mata a raga bayan da aka dawo daga hutu.

A wasan farko da aka buga Masar da Algeria tashi wasa kunnen doki suka yi.

Senegal ce ke karbar bakuncin wasannin matasa 'yan kasa da shekara 23, domin fitar da kasashe ukun da za su wakilci Afirka a wasan kwallon kafa da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.

Nigeria tana rukuni na biyu da ya kunshi Mali da Masar da Algeria, yayin da rukunin farko ke dauke da mai masaukin baki Senegal da Zambia da Afirka ta Kudu da kuma Tunisia.

Sai a ranar Talata ce za a cigaba da wasanni tsakanin Afirka ta Kudu da Zambi, sannan a kara tsakanin Tunisia da Senegal.