Ballon d'Or:Ronaldo da Messi da Neymar ke takara

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da Neymar ne 'yan wasa uku da ke takarar lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na bana, wato Ballon d'Or.

Wannan ce shekara ta takwas a jere da Ronaldo, dan kwallon Real Madrid, da dan wasan Barcelona Messi ke shiga cikin 'yan takara.

Wannan shi ne karon farko da Neymar ya shiga cikin jerin 'yan takara uku na karshe da za a zabi wanda ya fi yin fice a fagen tamaula a duniya.

Za a bayyana wanda ya lashe kyuatar bana ne a wani kasaitaccen biki da hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, za ta yi a Zurich a ranar 11 ga watan Janairun shekara mai zuwa.

An fitar da 'yan wasan uku ne daga cikin jerin 25 da tun a baya hukumar ta Fifa ta sanar ciki har da Gareth Bale dan wasan Real Madrid.