Liverpool ce ta fi biyan eja kudaden musayar 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Sakamakon kudaden da aka bai wa eja a gasar Premier tun daga bara

Liverpool ce kungiyar da take kan gaba wajen biyan wakilan 'yan wasan kwallon kafa ladan ciniki da ya kai fam miliyan 14 tun daga shekarar bara.

Hakan ne ya kuma sa aka kashe fam miliyan 129.86 fiye da fam miliyan 15 da aka biya wakilan wajen cinikayyar 'yan wasan tamaula a bara.

A manchester United kudin linkawa ya yi zuwa fam miliyan 14, yayin da Arsenal ta biya ninki uku da suka kai fam miliyan 12.

An yi jumullar kudaden da aka biya ne a Premier daga tsakanin 1 ga watan Oktoban 2014 zuwa 30 ga watan Satumba.

Ga jerin kudaden da kungiyoyin Premier suka biya eja tun daga bara:

 1. Liverpool £14,301,464 (£14,308,444)
 2. Manchester United £13,881,814 (£7,975,556)
 3. Manchester City £12,429,380 (£12,811,946)
 4. Chelsea £11,961,206 (£16,771,328)
 5. Arsenal £11,928,584 (£4,293,407)
 6. West Ham £7,049,001 (£6,380,339)
 7. Tottenham £5,987,052 (£10,983,011)
 8. Newcastle £5,946,031 (£3,876,250)
 9. Southampton £5,391,172 (£2,766,444)
 10. Stoke £5,308,545 (£3,986,850)
 11. Aston Villa £4,986,058 (£2,577,866)
 12. Crystal Palace £4,719,931 (£2,200,797)
 13. Everton £4,479,432 (£5,753,269)
 14. Swansea £4,250,030 (£3,784,090)
 15. Leicester £4,057,727 (£1,608,418)
 16. Sunderland £3,404,540 (£5,276,674)
 17. West Brom £3,342,217 (£3,493,745)
 18. Norwich City £2,484,285
 19. Bournemouth £2,328,862 (£709,231)
 20. Watford £1,620,229 (£355,750)