Me ke tsakanin Mourinho da Costa ?

Kocin Chelsea, Jose Mourinho ya ce ba shi da 'wata matsala' da Diego Costa bayan da ya ajiye dan kwallon a kan benci a wasansu da Tottenham.

An ajiye Costa a kan benci saboda ya zura kwallo daya tal ne a wasanni takwas da Chelsea ta buga, kuma ya nuna fushinsa inda ya wurga wa Mourinho rigar kwallo.

Mourinho ya ce "A gani na haka halinsa yake. Idan aka ajiye babban dan wasa a benci dole ne ya yi fushi."

"Idan yanason ya bata min rai ba haka zai yi ba.Ina dasawa da shi," in ji Mourinho.

Mourinho dai ya kare matsayinsa na ajiye Costa a benci a wasan da suka tashi babu ci a White Hart Lane, duk da cewar ya zura kwallo a wasansu da Norwich a makon da ya gabata.