Arsenal za ta auna girman raunin Sanchez

Hakkin mallakar hoto pa
Image caption Arsenal na fama da jerin 'yan wasanta da ke yin jinya

Arsenal za ta auna girman raunin da Alexis Sanchez ya ji nan da kwanaki biyu masu zuwa, domin sanin kwanakin da zai yi jinya.

Alexis Sanchez ya ji raunin ne a wasan Premier da Arsenal ta tashi kunnen doki 1-1 da Norwich City a filin wasa na Carrow Road ranar Lahadi.

Mai horas da Arsenal, Arsene Wenger, ya kare dalilin da ya sa ya saka dan kwallon wasa a ranar Lahadin, bayan da tun a wasan da suka yi da Dinamo Zagreb, Sanchez ya ji rauni.

Wenger ya ce bai yi niyyar saka shi a wasan Norwich ba, amma dai Sanchez ne da kansa ya ba shi tabbacin cewar zai iya buga wasan.

A kuma karawar da suka yi da Norwich din a ranar Lahadi Laurent Koscielny da Santi Cazorla su ma sun ji rauni, da hakan ya kara yawan 'yan kwallon Arsenal da ke yin jinya.

Jerin 'yan wasan Arsenal da ke yin jinya sun hada da Laurent Koscielny da Mikel Arteta da Francis Coquelin da Santi Cazorla da Tomas Rosicky da Jack Wilshere da Alexis Sanchez da Theo Walcott da kuma Danny Welbeck.