An kiyasta darajar Manchester City kudi £2bn

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City tana mataki na daya a kan teburin Premier

An kiyasta rukunin kamfanin Manchester City kan darajar kudi fam biliyon biyu, bayan da aka sayar da kashi 13 cikin dari na kamfanonin da ya kai kimanin kudin £265m.

An sayar da kashi 13 cikin dari na kamfanin ne ga masu zuba hannun jari na China da suka hada da China Media Capital (CFG) da kuma Citic Capital.

Tun a watanni shida da suka wuce ne suka fara tattaunawa a tsakaninsu da nufin fadada kamfanin Manchester City da cimma bukatunsa a fagen tamaula a China.

Za a kara bayar da wasu kason kamfanin Manchester City ga rukunin kamfanin CFG kari daga wajen mamallakinta mai rukunan kamfanin Abu Dhabi United.