Bility ya shigar da kara kan hana shi takarar Fifa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar 26 ga watan Fabrairu za a yi zaben shugaban hukumar Fifa

Musa Bility, ya shigar da kara a kotun da ke sauraren kararrakin wasanni, saboda cire sunansa da aka yi daga cikin 'yan takarar kujerar Fifa.

Kwamitin zabe na Fifa ne ya cire sunan shugaban na hukumar kwallon kafar Liberia daga jerin 'yan takara bisa cewar ba shi da mutuncin da ya kamata ya shugabanci hukumar.

Bility ya ce "Matakin da Fifa ta dauka bai kamata ba kuma babu adalci, batun ya kuma tsaya masa a rai domin abin takaici ne, saboda haka ya shigar da kara".

Shugaban mai shekara 48 ya yi kira ga kwamitin zaben na Fifa da ya auna mutuntakar sauran 'yan takara ya kuma sanar da sakamakon da ya samu ga mambobin hukumar su 209.

A ranar 26 ga watan Fabrairu a Zurich ake sa ran zaben sabon shugaban hukumar kwallon kafa na Fifa da zai maye gurbin Sepp Blatter, wanda aka dakatar a cikin watan Oktoba.

Ga jerin 'yan takarar da kwamitin zaben Fifa ya wanke:

  • Prince Ali bin al-Hussein
  • Sheikh Salman bin Ebrahim al-Khalifa
  • Jerome Champagne
  • Tokyo Sexwale