Ba mai farin ciki a Newcastle —McClaren

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Steve McClaren ya ce 'yan wasan Newcastle na cikin tashin hankali

Kocin Newcastle United, Steve McClaren, ya ce 'yan wasanshi ba su da kwarin gwiwa sosai yayin da suke shirye-shiryen tunkarar Liverpool ranar Lahadi a St James' Park.

Kungiyar ce dai ta 19 a teburin gasar Premier bayan kashin da ta sha makon jiya a hannun Crystal Palace, a wasan da suka tashi ci 5-1.

A cewar McClaren, "Babu wanda yake farin ciki a wannan kungiyar".

Ya kara da cewa, "Kwatsam sai ga shi mun yi taku uku mun matsa gaba, amma mun yi taku biyar ko shida mun koma baya".

Wasannin Premier biyu kawai kungiyar Newcastle ta lashe a cikin 14 da ta buga; a wannan tsakanin kuma an zura mata kwallaye 30 a raga.

Karin bayani