Rooney ya ji rauni a idon sawu

Image caption Ba a san ranar da Rooney zai koma taka leda ba

Kyaftin din Manchester United, Wayne Rooney zai yi jinyar rauni a idon sawunsa, abin da zai hana shi buga wasansu da West Ham a ranar Asabar.

Dan kwallon bai kammala wasansu da Leicester City ba a karshen makon da ya wuce saboda raunin.

Kocinsa Louis van Gaal ya ce tsakanin raunin ya wuce yadda suka za ta tun farko.

Van Gaal kuma ya tabbatar da cewar Marcos Rojo ya gurde a kafadarsa a lokacin atisaye.

Wasannin karshen mako a gasar Premier:

  • Stoke vs Man City
  • Arsenal vs Sunderland
  • Man Utd vs West Ham
  • Southampton vs Aston Villa
  • Swansea vs Leicester
  • Watford vs Norwich
  • West Brom vs Tottenham
  • Chelsea vs Bournemouth

Lahadi:

  • Newcastle vs Liverpool