Sakho zai yi jinyar watanni biyu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sakho ya bukaci a sauya shi

Dan kwallon West Ham, Diafra Sakho zai yi jinyar watanni biyu sakamakon rauni a cinyarsa a wasansu da West Brom.

Dan wasan mai shekaru 25, an cire shi daga wasan tun a minti na 17.

Kocin West Ham, Slaven Bilic ya ce "Tabbas zai yi jinyar makonni watakila hudu zuwa takwas, ko kuma fiye."

Dan kwallon na kasar Senegal, ya zura kwallaye biyar a wasanni 14 a kakar wasa ta bana.

Wasu 'yan wasan West Ham da ke jinya sun hada da Dimitri Payet da kuma Enner Valencia.