Rojo ya ji tagarde a kafadarsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A kakar wasa ta bana, Marcos Rojo bai haskaka ba sosai

Dan kwallon Manchester United, Marcos Rojo zai yi doguwar jinya bayan da ya yi targade a kafadarsa a lokacin horo.

Lamarin ya faru ne a ranar Laraba, kuma a nan bangaren jikinsa ne, Rojo ya ji rauni a wasansu da Manchester City a kakar wasan da ta wuce.

A wancan lokacin, Rojo mai shekaru 25, ya yi jinyar makonni hudu.

Ana sa ran nan gaba kocin United, Louis van Gaal zai bayyana tsananin raunin da Rojo ya ji.

A shekarar 2014, Rojo ya koma United daga Sporting Lisbon a kan fan miliyan 16.