Bournemouth ta doke Chelsea a Stamford Bridge

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Karo na takwas kenan da ake cin Chelsea a Premier

Chelsea ta yi rashin nasara a hannun Bournemouth da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a Stamford Bridge a ranar Asabar.

Glenn Murray ne ya ci wa Bournemouth kwallo a wasan saura minti takwas a tashi daga fafatawar.

Wannan shi ne wasa na takwas da aka ci Chelsea a gasar Premier, bayan wasanni 15 da ta buga, inda ta ci fafatawa 4 ta kuma buga canjaras a wasanni 3.

Chelsea tana nan da makinta 15, yayin da Bournemouth ta hada maki 13.