An kori Real Madrid daga gasar Copa del Rey

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid ta karbo Denis Cheryshev daga Villareal wacce ya buga wa wasanni aro

Hukumar kwallon kafar Spaniya ta kori Real Madrid daga gasar Copa del Rey, sakamakon samunta da laifin saka dan wasan da bai dace ba a karawar da suka yi da Cadiz.

A ranar Laraba ce Real Madrid ta doke Cadiz da ci 3-1 a wasan kungiyoyi 32 da suka rage a gasar, wanda Denis Cheryshev ne ya fara ci mata kwallo a karawar.

Denis Cheryshev, dan kasar Rasha bai kamata ya buga karawar ba, domin ya kamata ya huta a wasa daya, sakamakon hukunta shi da aka yi lokacin yana wasa aro a Villareal.

Real Madrid ta ce za ta dauki duk wasu matakan da suka dace domin a tabbatar da cewa an yi mata adalci.

Real ta lashe Copa del Rey sau 19, wanda rabon da ta dauki kofin tun a shekarar 2014.