Stoke City ta ci Manchester City 2-0

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Karo na hudu kenan da aka ci Manchester City a gasar Premier bana

Stoke City ta doke Manchester City da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a filin wasa na Britannia ranar Asabar.

Marko Arnautovic ne ya fara cin kwallo a minti na bakwai da fara tamaula, sannan ya kara ta biyu a minti na 15 da fara fafatawar.

Manchester City wacce ke mataki na daya a kan teburin Premier kafin wasan mako na 15, ta buga karawa da Stoke ba tare da Sergio Aguero da Yaya Toure, wadanda ke yin jinya.

Da wannan sakamakon Manchester City ta hada maki 29 bayan buga wasanni 15, yayin da Stoke City ke da maki 22.