Ibrahimovic ya kafa tarihin cin kwallaye a PSG

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption PSG ce ke kan gaba a kan teburin gasar Faransa

Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasan Paris St-Germain da yafi yawan ci wa kungiyar kwalllaye a gasar kasar Faransa ta Ligue 1.

Ibrahimovich, ya kafa tarihin ne, bayan da ya ci Nice kwallaye biyu a wasan Ligue 1 gasar mako na 17 da suka samu nasara da ci 3-0 a ranar Juma'a.

Edison Cabani ne ya fara cin kwallon, sannan Ibrahimovich ya ci ta biyu daga bugun fenariti daf da za a tafi hutu, sannan ya kara ta uku a raga a minti na 61.

Hakan ne ya kuma sa ya dara Mustapha Dahleb da kwallo daya, wanda ya ci wa PSG kwallaye 86 a wasannin 306 da ya buga mata tamaula.

PSG ta buga wasanni 17 a gasar ta kasar Faransa ba a doke ta ba a bana, wanda rabon da a samu nasara a kanta tun a ranar 15 ga watan Maris.

Hakan ne ya kuma sa ta hada maki 45 daga wasanni 17 da ta buga, wanda take shirin lashe kofin gasar Faransa karo na hudu a jere.