"Platini yana da shaidar yin gaskiya a Fifa"

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A shekarar 2011 ne Blatter ya biya Platini kudin ladan aikin da aka yi masa

Lauyan Michel Platini ya ce wata yarjejeniyar da aka wallafa tsakanin Blatter da Platini a wata jaridar kasar Faransa za ta taimaka wajen wanke shi kan zargin da ake yi masa.

Jaridar Le Journal du Dimanche ya ce yarjejeniyar da suka kulla ta biyan Platini ladan aiki da ya yi wa Blatter a 1998, zai warware zargin cin hanci da ake yi masa.

Tun a cikin watan Oktoba kwamitin da'a na hukumar ta Fifa ya dakatar da Blatter da Platini daga shiga harkokin wasanni, saboda zargin cin hanci da rashawa.

Lauyan na Platini, Thomas Clay ya ce shaidar yarjejeniyar da suka kulla a tsakaninsu wata muhimmiyar shaida ce a wajensu da za su wanke laifin da ake zarginsu.

Ya kuma kara da cewar da zarar sun gabatar musu da shaidar, za a kawo karshen zargin da ake yi wa Platini.