Newcastle United ta ci Liverpool 2-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki 23

Newcastle United ta doke Liverpool da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a St James Park ranar Lahadi.

Newcastle ta ci kwallon farko inda Martin Skrtel ya ci gida daga bugun da Georginio Wijnaldum ya yi wo ta bugi gwiwar kafarsa ta fada raga.

Wijnaldum dan kwallon tawagar Netherlands din ne ya ci ta biyu daf da za a tashi daga fafatawar.

Wannan shi ne karo na hudu da aka doke Liverpool a gasar Premier, inda ta ci karawa 6 ta kuma buga canjaras a fafatawa 5 daga cikin wasannin 15 da ta buga a gasar ta Premier.

Ita kuwa Newcastle wacce ta samu maki uku a kan Liverpool ta koma mataki na 18 a kan teburi da maki 13.