Kan 'yan wasan Madrid a hade yake - Bale

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana mataki na uku a kan teburi da maki 30

Gareth Bale ya ce kungiyar Real Madrid kanta a hade yake duk da dan koma baya da ta fuskanta a makonnin da suka wuce.

Real Madrid ta sha kashi a hannun Barcelona da ci 4-0 a gasar La Liga a Bernabeu, sannan aka kore ta daga Copa del Rey, bayan da aka sameta da laifin yin amfani da dan wasan da bai dace ba.

A ranar Asabar ne Real Madrid ta ci Getafe 4-1, wanda hakan ya sa sauran tazarar maki hudu ya rage tsakaninta da Barcelona wacce ke mataki na daya a kan teburin La Liga.

Bale ya ce "Abu mafi mahimmanci shi ne da kan 'yan wasa yake a hade, za kuma mu lashe wasanni domin kare yin fice a tamaula".

A ranar Laraba ne hukumar kwallon kafar Spaniya ta kori Madrid bisa saka Denis Cheryshev a karawar da ta yi da Cadiz a gasar Copa del Rey.