Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 26 zuwa Super Eagles

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Za a fara wasannin cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke taka leda a gida a Rwanda

Sunday Oliseh ya gayyaci 'yan wasa 26 domin fara atisayen tunkarar gasar kwallon kafa ta cin kofin Afirka ta 'yan wasan da suke taka leda a gida da za a yi a Rwanda a 2016.

Tuni aka raba jadawalin da ya kunshi tawagar kwallon kafa ta Super Eagles da take a rukuni na uku da ya kunshi Nijar da Tunisia da kuma Guinea.

Oliseh ya umarci 'yan wasan da ya gayyata da su halarci otal din Bolton White Apartments da ke Abuja a ranar Litinin 14 ga watan Disamba.

Za a fara gasar cin kofin Afirka karo na hutu ta 'yan wasan da suke taka leda a gida daga tsakanin 16 ga watan Janairu zuwa bakwai ga watan Fabrairun 2016.

Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata Super Eagles:

Masu tsaron raga: Ikechukwu Ezenwa (Sunshine Stars); Olufemi Thomas (Enyimba FC); David Obiazor (Heartland FC); Okiemute Odah (Warri Wolves)

Masu tsaron baya: Kalu Orji (Enugu Rangers); Austin Oboroakpo (Warri Wolves); Jamiu Alimi (Shooting Stars); Matthew Etim (Enugu Rangers); Stephen Eze (Sunshine Stars); Chima Akas (Sharks FC); Chris Madaki (Giwa FC)

Masu wasan tsakiya: Ifeanyi Matthew (El-Kanemi Warriors); Paul Onobi (Sunshine Stars); Usman Mohammed (FC Taraba); Bature Yaro (Nasarawa United); Osas Okoro (Enugu Rangers); Bartholomew Ibenegbu (Warri Wolves); Julius Ubido (Heartland FC); Ibrahim Salawa Attah (Shooting Stars); Christian Madu (Enugu Rangers)

Masu cin kwallaye: Ezekiel Bassey (Enyimba FC); Gbolahan Salami (Warri Wolves); Tunde Adeniji (Sunshine Stars); Bright Onyedikachi (FC IfeanyiUbah); Chisom Chikatara (Abia Warriors); Prince Aggreh (Sunshine Stars)