Za a ci gaba da buga tamaula a Saliyo

Hakkin mallakar hoto Sta Kambou Getty
Image caption Caf ta amince da Saliyo ta karbi bakuncin wasan kwallon kafa a gidanta

Kasar Saliyo za ta dawo da karbar bakuncin manyan wasannin kwallon kafa, bayan da aka wanke kasar daga cikin masu dauke da cutar Ebola.

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ce ta dakatar da Saliyo daga karbar bakuncin wasanni a kasarta, kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta umarta da a yi.

Saliyo wadda aka dakatar daga karbar bakuncin wasannin tamaula a Agustan 2014, za ta iya saukar bakin tawagar kwallon kafa a kasar, bayan da aka cire ta daga jerin masu dauke da cutar Ebola.

Kasar Liberia da Guinea suna daga cikin jerin tawagar kwallon kafa da hukumar Caf ta dakatar daga karbar wasan kwallon kafa domin kaucewa yada cutar Ebola.

Koda yake Caf ta amince da Liberia da ta ci gaba da buga wasannin tamaula, har yanzu ba a bai wa Guinea izini ba sakamakon rashin wanke ta daga hukumar lafiya ta duniya.