Ba za a kore ni daga Chelsea ba - Mourinho

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Chelsea za ta kara da FC Porto a ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai

Kociyan Chelsea, Jose Mourinho, ya ce yana da tabbacin cewa Roman Abramovich, ba zai kore shi daga aiki ba, duk da rashin kokarin da yake yi a wasannin bana.

Chelsea wadda ta lashe kofin Premier bara, tana mataki na 14 a kan teburin gasar bana, kuma an doke ta wasanni takwas a Premier an kuma cire ta daga League Cup.

Da aka tambaye shi ko mai ya sa ba za a kore shi daga Stamford Bridge ba, sai ya ce saboda ya samar wa da kungiyar nasarori.

Mourinho ya koma Chelsea da horas da tamaula a karo na biyu a shekarar 2013, inda ya lashe kofin Premier da na Capital One Cup.

A kuma lokacin farko da ya fara jan ragamar kungiyar daga tsakanin 2004 zuwa 2007 ya dauki kofunan Premier biyu da FA da kuma kofunan League Cup biyu.