Neymar ne dan kwallon da ya fi fice a Nuwamba a Spain

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A watan Satumbar 2013 aka fara bayar da kyautar dan wasan da ya fi yin fice a La Liga

A karon farko Neymar, ya lashe kyautar dan kwallon da ya fi yin fice a watan Nuwamba a gasar La Liga ta Spaniya.

Neymar ya zama dan wasan Barcelona na farko da ya fara lashe kyautar da aka fara gudanar da ita a watan Satumbar 2013.

Dan wasan ya ci kwallaye biyar a wasanni uku da ya buga a watan jiya, dalilin da ya sa alkalan da ke kula da kyautar suka zabe shi.

Dan kwallon Real Madrid, Cristiano Ronaldo, yana daga cikin 'yan wasa biyar da suka lashe kyautar sau biyu.

'Yan kwallon da suka samu kyautar sau daya sun hada da 'yan wasan Athletico Madrid, Diego Godin da Antoine Griezmann da Nolito na Celta Viga da kuma Carlos Vela na Real Sociedad